Silva zai ci gaba da taka leda kaka daya a Manchester City

Bernardo Silva

Asalin hoton, Getty Images

Bernardo Silva ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya domin ya ci gaba da taka leda a Manchester City.

Kenan kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2026, bayan da tun farko yarjejeniyar dan kwallon tawagar Portugal za ta karkare a 2025..

Kaka biyu baya da ta wuce an yi ta alakanta Silva, mai shekara 29 da cewar zai koma Barcelona, wasu kuma na cewar Paris St-Germain ko Al-Hilal zai koma.

Silva yana cikin 'yan wasan da suka ci wa City kofin Premier League biyar tun bayan da ya koma kungiyar a Mayun 2017.

Pep Guradiola ya rasa 'yan wasa biyu a kakar, bayan da Ilkay Gundogan ya koma Barcelona shi kuwa Riyad Mahrez ya je Al-Ahli mai buga gasar Saudi Arabia.

Sai dai kociyan ya dauki mai buga tsakiya a bana wato Mateo Kovacic daga Chelsea, ta kuma kulla yarjejeniyar daukar Jeremy Doku daga Rennes.

Silva ya ci kwallo bakwai da bayar da takwas aka zura a raga a wasa 55 da ya buga a bara, kakar da City ta lashe kofi uku wato Premier League da Champions League da kuma FA Cup.

City wadda ta yi rashin nasara a Community Shield a hannun Arsenal a bugun fenariti ta lashe Uefa Super Cup, bayan cin Sevilla 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.